Rann dai shelkwatar Kala Balgene kusa da Tafkin Chadi kuma 'yan Kilomitoci kadan ne tsakaninsa da Gamborun Ngala.
Rahotanni sun ce matasan sun kwace babura 70 na 'yan Boko Haram kuma sun kwace motoci biyu kirar Hilux an kuma kama wasu daga cikin maharan.
Makon da ya gabata dai 'yan Boko Haram sun kai farmaki Gamborun Nagal makwabciyar Kala Balgen inda suka kashe mutane sama da dari uku.ABNA.